Kungiyar Masu Siyar Da Kayan Gwari Dake Jihar Gombe Ta Koka Kan Yadda Ake Raba Naira Miliyan 500 Da Gwamnan Jihar Gombe Ya Bawa 'Yan Kasuwa
A yau Litinin kungiyar 'yan Gwari masu saida kayan Gwari da suka hada da; Tumatur, Albasa, Tattasai, Attarugu da sauran kayayyaki reshen jihar Gombe karkashin jagorancin shugaban kungiyar na jihar Gombe Alhaji Sani Waya, ta koka kan yadda aka maida kungiyar saniyar ware wurin raba tallafin kudaden da Gwamnan jihar ya bayar domin a rabawa kungiyoyin 'yan kasuwa wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban kungiyar ya shaidawa wakilin mu da cewa a yau aka turo musu da Fom guda 50 mai dauke da mutum Goma a kowane Fom guda da sunan za'a bada Naira dubu 20 a kowane Fom, inda kowane mutum za'a bashi Naira dubu biyu, jadawalin lissafin ya kama Naira Miliyan Guda za'a bawa 'yan kungiyar dake fadin jihar Gombe da sauran kananan hukumomi baki daya.
Rabon kungiyar da ta samu gudummuwa tun lokacin mulkin tsohon Gwamnan jihar Gombe Sanata Muhammad Danjuma Goje, wanda a wancan lokacin duk shekara kungiyar tana samun gudummuwa kusan sau biyu na kayayyakin abinci, taki, da kudade.
Daga karshe kungiyar ta yiwa Gwamnan jihar Gombe fatan sake lashe zabe a karo na biyu da kuma mika sakon godiyarsu ga kungiyar AMATA na chanja musu suna da tayi, sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta duba tsarin rabon kudin da yadda aka maida kungiyar saniyar ware duk da yawan da suke dashi a fadin jihar.
Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku