Babu abu mafi saurin rudar da mutum ya sauya masa tunani a lokaci gudu kamar irin rayuwar social media, Domin mafi yawan jamma a ko kaso na abin da ake rubutuwa ko yadawa ba gaskiya ba ne a wasu kafafen yada labarai.
Dan uwa kula yi hankali da abin da kake gani, kuma kayi duban tsanaki, kabi abin da zaka karu. Domin da dama sun bi a makance an rufta su, ba su kare a matattara mai kyau ba, Allah yarufa asiri.
Wajibi ka sakawa kanka linzami, in kana bibiyar masu rubuce rubuce a social media, Da ka ga anyi in da hankalinka bai kwantaba da shiba kawai anzo wurin da zaka sauka.
Idan kuwa ka biyewa musu to ba za ayi nisa ba, zaka gane ka fada cikin haÉ—ari sai kayi nisa.
Social media wata matattara ce da ke dauke hankalin mafi yawan mutane daga gaskiya zuwa karya. Lokacin guda take sauya fasalin marasa lissafin cikinmu su fara sabuwar dabi’u su manta asalin su waye ne su a rayuwa.
Ga misalai nan kamar hakan
Yakamata Mu maida hankalin mu ga ingantattu shafuka masu yada gaskiya da alhairi, kamar haka.
- Ilimin Addini
- Ilimin zamani
- Sahihan Labarai duniya daga sanannu gidajen jarida
- Harkar Lafiya
- Saye da sayarwa da Kasuwanci
A cikin wadannan bayanen Ina da yakinin zamu samu riba mai anfani, maimakon biye masu yada Karya, gaba, kiyayya, shedanci, shashanci da farfa ganda Al’umma mu.
Allah ya bamu ikon yada alkairi, Ameen
Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku