CSO ta kai karar gwamnoni 4 tare da Jami’an INEC 44, da wasu mutum 26 bisa zargin su da magudin zabe na 2023

 


CSO ta kai karar gwamnoni 4 tare da Jami’an INEC 44, da wasu mutum 26 bisa zargin su da magudin zabe na 2023


 Wata kungiyar farar hula, International Society for Civil Liberties da Rule of Law (Intersociety) ta kai karar manya jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) 44 da hannu a cikin zargin magudin cikin gida na jihohi INEC na zaben shugaban kasa. 

manyan ofisoshin jakadanci na kasashen waje a Najeriya, masu wakiltar mafi kyawun dimokuradiyya na duniya.

 Har ila yau, sun garzaya da su gaban kasashe talatin da daya da ake mutunta tsarin dimokuradiyya a duniya don dakile masu magudin Zabe,da zargin magudin zabe a cikin gida da kuma cin zarafin jama’a da akeyi, an zargi gwamnonin jihohi hudu da hannu cikin cin zarafin mutane yayin kada kuri'u.Kasashen duniya da aka rubuta musu korafin sun hada da, shugaban tawagar EU a Najeriya  ECOWAS da jakadu manyan kwamishinonin Amurka, Birtaniya, Kanada, Faransa, Jamus, Isra'ila, Italiya, Switzerland, Belgium, Denmark, Scotland da Ireland.Sauran su ne Spain, Czech, Portugal, Norway, Finland, Austria, Netherlands, Sweden, Poland, Girka, Hungary, Bulgaria, Slovakia, Australia, Vatican, Koriya ta Kudu, Brazil da Mexico.

 Wadanda suka shigar da kara kan laifin cin hanci da rashawa ko kuma kai tsaye a cikin wasikar ta Intersociety sune Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC na kasa da mutum goma sha hudu masu rike da mukamin kwamishinonin hukumar na kasa - tare da jihohinsu na asali.

 Ga jerin sunayensu 

RTD Air Vice Marshal Ahmed Mua'zu, Gombe, Mrs May Agbamuche Mbu Delta,Dr Adekunle Ladipo Ogunmola Oyo, Mallam Mohammed Kudu Haruna "Kano",Ukegbu Nnamdi (Abia), Rtd Major Gen Abubakar Alkali Adamawa da Rhoda Gumus Bayelsa.Haka kuma akwai Sam Olumekun "Ondo" Barr Festus Okoye "Anambra", Kunle Ajayi "Ekiti", Muhammad Kallah "Borno" da kuma Dr Baba Bila "Arewa maso Gabas", Farfesa Sani Adam "Arewa Ta Tsakiya" da kuma Farfesa Abdullahi Abdu "Arewa Yamma". Su ne a shigar da kararsu a gaban kasashe masu mutunta Demokra diyya a duniyar yau.

Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku