Auran mata 2 atare: Ina jin kamar ina aljanna In ji cewar matashin da ya auri mata 2 a rana daya

 


Auran mata 2 atare: Ina jin kamar ina aljanna In ji cewar matashin da ya auri mata 2 a rana daya


Anyi abun mama ki, Wani matashi mai suna Umar Sani da ya auri mata biyu a rana guda a garin Minna na jihar Neja, ya ce yana ji kamar yana aljanna.Sani wanda ya auri Safiyya Tanimu Nasidi da Maryam Yusuf Galadima a ranar Juma’a, ya shaida wa Shafin Tsalle Daya cewa Ina ji kamar an ba ni gida a aljanna ina godiya ga Allah matuka sannan ina cikin fari ciki mara misaltuwa.

Ni Na gode wa Allah da ya cika min burina na auri mata biyu a rana daya. Dukansu kuma suna da fahimta. Ina matukar godiya da hakan.Mutane da yawa sun yi tunanin cewa za a sami matsala daga É—ayansu amma Allah  cikin ikon Allah da hikimarsa ya sa aka yi komai lafiya da fatan alheri.

Umar ya bayyana cewa shi ya kudiri niyar yin hakan ne saboda ya taso a gidan su da ya tarar da mata mahaifin sa fiye da daya ne shiya sa ya kudira zaiyi shima.

Tun ina É—an shekara goma na ga mahaifina yana da mata huÉ—u kuma na ga yadda suke zaman lafiya. Na yi wa kaina alkawari zan auri mata fiye da daya idan na samu hanya, ko in yi aure uku ko hudu a rana guda.


Ko da yake ya ce iyayensa sun yi mamakin shawarar, amma ba su hana shi cika burinsa ba.Iyayena sun yi mamaki domin ko mahaifina bai auri mata biyu a rana daya ba. Amma ba su yi ki amincewa da hakan ba, Abu mafi muhimmanci a gare mu a yanzu shi ne Allah ya bamu zaman lafiya inji shi.

Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku