ABU zariya: za ta ƙirƙiro mota mai amfani da ruwa a madadin fetur a 2023
Shugaban tsangayar ilimin fasaha a Jami’ar Ahmadu Bello ABU Zariya, da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Dabo yaci gaba cewa jami’ar na shirye-shiryen kera wata mota, kirar gida Nijeriya da za ta rika amfani da ruwa a maimakon a zuba mata fetur sai tayi aiki da shi.
Shugaban ya bayyana haka ne a jiya Asabar a birnin Zariya, A yayin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙas a kan bikin ranar Injiniyanci ta Duniya na 2023 don samun ci gaba mai dorewar ayyukan motar.
Farfesa Dabo, ya ce an samu ci gaba so sai da dama a ABU, A ciki har da samar da wata motar tsere, don ingantata yan da yakamata.
A nan ne ya kara da cewa jami’ar tana aikin samar da wata motar da za ta rika tafiyar da ruwa maimakon man fetur, a tsarin motar.
Ita Motar tseren da jami'ar ta kera tana da karfin tafiyar kilomita 100 a kan litar mai ɗaya kadai, a jawa bin nashi dake bayarwa.
A Fadar/cewarsa' an kai wannan motar zuwa Afirka ta Kudu inda kuma tana nan ta na aiki yadda ya kamata acikin Al'umma.
Ya kuma kara da jaddada cewa jami’ar tana kokarin inganta shan man motar ne.
Ma'anar motar wata karamar mota wace da ke daukar mafi yawan cin mutane guda biyu da sirdi don gasar tsere a wasu yan kunan, ba don zirga-zirgar jama'a na yau da kullum ba ne, a fadar sa yan da motar zata kasance.
Kuciga da bibiyar domin ingantattun labarai da-dumi dumin su muna Godiya.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku