Naurar BVAS ta kasa ba da izinin wa matar Wike, a wurin kada Kuri'u

 


Bayan ya tsaya na kusan mintuna 25, Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya kasa samun sahihancin kada kuri’arsa a mazabar sa ta 8, Ward tara, Rumueprikon, Obio-Akpor, biyo bayan gazawar tsarin tantance masu kada kuri’a na Bio-modal (BVAS).

Gwamnan tare da mai dakin sa Suzzette sun bar rumfar zabe da misalin karfe 11 na safe yayin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) suka roke su da su dakata kadan. Jami’an sun bayyana rashin nasarar BVAS a matsayin babbar matsala a jihar, inda suka kara da cewa suna jiran kwararrun da aka tura sashin domin gyara matsalar.

Taron masu kada kuri'a sun yi hakuri suna jiran fara tantancewa a sashin. Gwamnan wanda ya bar sashin ya ce sun ji takaicin INEC. Ya ce: “Mun ji takaici matuka, INEC ta ce mana sun shirya zabe kuma BVAS na aiki, za ka ga jama’a a nan, ba na tunanin za a bar yawancin mutane su kada kuri’a tare da tafiyar hawainiya da BVAS. “Na dau kusan mintuna 25 a nan, sai aka ce in je in dawo, za su gyara BVAS. Mun yi matukar takaici. Idan da yawan mutane ba su da hakki, me kuke tsammani.

"Mutane za su yi fushi kuma komai na iya faruwa, ya kamata INEC ta shirya tsaf kafin ta fada wa jama'a cewa a shirye suke, babu tashin hankali a ko'ina a jihar".






0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku