Bayanin jarumin kannywood kenan kan zabe gobe :Falalu A Daurayi

 


Gobe Zabe In shaa Allah.

Rana ce da zamuyi amfani da kuriarmu mu zabi cancanta domin shimfida makomar kasarmu a hannu nagari.

Wajibi ne muyi amfani da wannan damar muyi duba tsanaki mu zabi nagartaccen Jagora domin amfaninsa da alkairinsa ga al’umma.


Mu zabi Jagora wanda zai aiki da dukiyar kasa wajan kawo karshen matsalolin da suke addabar mu Arewa da Kudu ba wanda zai raba dukiyar ga iyalansa da Yan korensa ba.


Lallai mu sani zaben baragurbi kamar mun sake saka makomarku ta shekaru fudu ne a kila wa kala da danasani.  

Ita kuwa tafiyar kila wa kala da danasani dai dai take da tafiya cikin duhu ga makaho babu Danjagora. Allah ya kyauta.


Su Kuma Shugabanni wadanda za’a zaba, wajibinsu ne su dinga kallon gefan masu kushe su, cikin kushen za su iya cin karo da abin da aka fada gaskiya ne sai suyi amfani da shi wajan gyaran mulkinsu. Idan kuma karya ake musu sun sami kankarar zunubi, domin ba duka shugaba mutanen jikinsa suke gayamar gaskiya ba.




Allah ka taimakemu ka bamu Jagara nagari. Amin Barkanmu da Juma’a Brothers & Sisters.

0 Comments

Ku Fadi Ra'ayinku