Wata Rana Wani Mutum Ya ga dansa Da Bai Wuce Shekaru Bakwai(07) Ba Yana Wani Zane a Kan Takarda, Sai Ya Zo Ya Zauna a Kusa Da Shi Yana Tambayarsa Cikin Nishadi.
Me Kake Zana Mana Ne?
Yaro Ya Ce,Ai Gidana Ne Baba.
Ya Ce,Masha ALLAH! Sannan"Baban" Ya Nuna Wani Babban Wuri a Cikin Zanen.
Nan Ina Ne?
Yaron Ya Ce,Dakina Ne.
Nan Fa?
Yaro Ya Ce,Dakin Matata Ne.
Uban Ya Yi Dariya. Sannan Ya Kara Nuna Wani. Wannan Fa?
Ya Ce,Na Yarana Ne.
Sanan Ya Nuna Wani Dan Wuri Mafi Kankanta Acan Gefe. Ya Tambayi Yaron, To Nan Bandaki Ne?
Sai Yaro Ya Ce Dakinka Ne.
Sai Uban Ya Ji Wani Iri Sannan Ya Dubi Yaron Cikin Damuwa.
Kai Yanzu Duk Girman Gidan Nan Da Dakunan Da Ka Zanawa Mutane Ni Dan Wannan Za Ka Iya Ba Ni?
Sai Yaron Ya Ce Masa Abba Ai Na Ga Shi Ma KAKA a Gidan Nan Duk Dakinsa Shi Ne Mafi Kankanta Kuma Acan Waje 'Daya Ba Kowa a Kusa Da Shi
Sannan Ne Mutumin Ya Tuno a Irin Yanayin Da Ya Ajiye Nasa MAHAIFINSA a Gidan.
Abin Da Ka Shuka.
Duk wada yayi wani abu marar kyeu shi zai girbi kayan sa tayau da kullum wanna shiya ake so mutu yarin ka abu mai kyeu.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku