Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya mayar da martani kan abubuwan da suka faru bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar PDP.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a filin jirgin sama na Fatakwal da ke babban birnin jihar Ribas jim kadan bayan dawowarsa daga wata kasar waje.
"Na yanke shawarar yin shiru ne saboda PDP jam'iyya ce da nake so sosai," in ji gwamnan yayin ganawa da manema labarai. “Na ci gaba da kulla yarjejeniya ta zamantakewa da mutanen Rivers. Duk da haka, lokaci ya yi da za a sanar da ‘yan Nijeriya gaskiyar lamarin.”
Gwamna Wike ya caccaki jawabin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar da ya bayyana Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.
Ya kuma zargi tsohon mataimakin shugaban kasar da yin karya a kansa, tare da yin amfani da wasu jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa wajen yada karya a kan mutumin nasa.
Gwamnan ya sha alwashin mayar da martani ga duka mai rike da tutar jam’iyyar da kuma jiga-jigan jam’iyyar da ya bayyana a matsayin ‘karnukan kai hari’ Atiku daya-bayan-daya da layi-layi a lokacin da ya dace.
Ya ce ‘yan baya ba za su yafe masa ba idan har ya kasa kafa tarihi sannan kuma ya yi alkawarin kawar da kai bayan kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar za ta kaddamar.

0 Comments
Ku Fadi Ra'ayinku